Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen Jihar Kebbi ta yi Allah-wadai da lalata allunan kamfen da fastocinta a garuruwan Argungu da Birnin Kebbi, inda ta zargi wasu da ake kyautata zaton magoya bayan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ne da hannu a lamarin. Sakataren Yada Labarai na APC a jihar, Alhaji Isah Abubakar […]
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen Jihar Kebbi ta yi Allah-wadai da lalata allunan kamfen da fastocinta a garuruwan Argungu da Birnin Kebbi, inda ta zargi wasu da ake kyautata zaton magoya bayan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ne da hannu a lamarin.
Sakataren Yada Labarai na APC a jihar, Alhaji Isah Abubakar Assalafi, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da bai kamata ba, yana mai gargadin cewa bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya haifar da tashin hankali, tsoratarwa ko lalata dukiyoyin wasu ba.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Assalafi ya ce ya kamata jam’iyyun siyasa su mayar da hankali wajen bayyana manufofinsu, nasarorinsu da shirye-shiryensu ga al’umma, maimakon aikata abubuwan da za su iya kawo cikas ga zaman lafiya da gudanar da harkokin dimokuradiyya.
Ya jaddada cewa kowace jam’iyyar siyasa tana da ‘yancin gudanar da halastattun ayyukanta, ciki har da lika fastoci da kafa allunan kamfen, ba tare da tsangwama ko barazana ba.
A cewarsa, gwamnatin Jihar Kebbi karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta APC na ci gaba da mutunta doka da oda, zaman lafiya da ka’idojin dimokuradiyya.
Kakakin APC ya bukaci magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankalinsu tare da kauce wa daukar fansa, yana mai kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike kan zargin lalata kayan kamfen din tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a gaban shari’a.
Haka kuma, Assalafi ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar ADC da su ja kunnen magoya bayansu domin kauce wa duk wani mataki da zai iya haifar da rikicin siyasa.
Ya ce bambancin ra’ayi da fafatawar neman goyon bayan jama’a bai kamata su zama dalilin lalata dukiyoyin jam’iyyun hamayya ba.
Assalafi ya sake tabbatar da kudurin APC na gudanar da harkokin siyasa cikin lumana, mutunta hakkokin sauran jam’iyyu da kuma tabbatar da dorewar zaman lafiya a fadin Jihar Kebbi.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu damar tabbatar da sahihancin zargin da ake yi wa magoya bayan ADC daga wata majiya mai zaman kanta ba, yayin da kuma ba a samu martanin jam’iyyar ADC kan zargin ba.
Brinkle FM 93.9 Zuru — Fiye da Rediyo, Muna Hada Ku da Duniya.
