Tsofaffin sojojin Najeriya sun toshe kofar shiga ofishin Hukumar Kula da Fanshon Sojoji da ke babban birnin ƙasar Abuja a ranar Talata, domin neman a biya musu buƙatunsu na sauya tsarin da aka amince da shi wajen biyansu kuɗaden fanshonsu. Tsofaffin sojojin sun yi zaman dirshen a kofar shiga ofishin, yayin da sojoji masu […]
Tsofaffin sojojin Najeriya sun toshe kofar shiga ofishin Hukumar Kula da Fanshon Sojoji da ke babban birnin ƙasar Abuja a ranar Talata, domin neman a biya musu buƙatunsu na sauya tsarin da aka amince da shi wajen biyansu kuɗaden fanshonsu.
Tsofaffin sojojin sun yi zaman dirshen a kofar shiga ofishin, yayin da sojoji masu ɗauke da makamai suka tare kofar shiga harabar ofishin, kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito.
Wannan alamari na zuwa ne makonni bayan zanga zangar da wasu tsofaffin sojojin suka gudanar a Ma’aikatar Tsaro a watan Satumba, inda suka buƙaci a ƙara musu kuɗaden fansho bayan ƙarin albashin da aka yi wa sojojin da ke aiki.
Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya yi alƙawarin cewa wadanda suka yi ritayar za su samu karin kudin fansho a watan Oktoba.
Shugaban Kungiyar Tsofaffin Sojojin Najeriya, Laftanar Kanal Innocent Azubike, ya zargi hukumar da amfani da tsarin lissafa fansho wanda a cewarsa, bai yi dai dai da abin da ya kamata a rika biyansu ba.
