Mazauna Jihar Kebbi sun toshe babbar hanyar Jega zuwa Kontagora a ranar Asabar domin nuna adawa da hare-haren da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne ke kai wa al’ummomin karkara, lamarin da ya tilasta wa iyalai barin gidajensu tare da kawo cikas ga ayyukan noma. Zanga-zangar ta jawo tsaiko ga matafiya da direbobi na […]
Mazauna Jihar Kebbi sun toshe babbar hanyar Jega zuwa Kontagora a ranar Asabar domin nuna adawa da hare-haren da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne ke kai wa al’ummomin karkara, lamarin da ya tilasta wa iyalai barin gidajensu tare da kawo cikas ga ayyukan noma.
Zanga-zangar ta jawo tsaiko ga matafiya da direbobi na tsawon sa’o’i, yayin da masu zanga-zangar suka kunna wuta a kan hanyar duk da ƙoƙarin da ’yan sanda suka yi na tarwatsa su ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Wani mazaunin Jega, Nazeer Muhammad, ya shaida wa jaridar cewa hare-haren da ake ta kai wa sun tilasta wa mazauna wasu ƙauyuka barin gidajensu. Ya ce wasu iyalai da suka rasa matsugunansu sun fito ne daga Mayama da Ungushi, da ke maƙwabciyar Jihar Sakkwato.
Wani mazaunin yankin mai suna Malam Idris ya ce kusan manyan motoci takwas ɗauke da mutanen da suka rasa matsugunansu sun isa Jega a ranar Lahadi. A halin yanzu, wasu daga cikin iyalan suna zaune a makarantu, yayin da wasu ke fama da rashin matsuguni kuma suke dogaro da taimakon al’ummar yankin.
Tun da farko, mazauna Alelu, Kimba, Jandutsi da Jadadi, da ke Ƙaramar Hukumar Jega, sun yi kira ga Gwamna Nasir Idris da ya gaggauta ɗaukar matakan magance matsalar tsaro.
A wata wasiƙa ta buɗe da aka rubuta ranar 9 ga Oktoba, wani mazaunin Alelu mai suna Sufiyan ya buƙaci a kafa sansanonin jami’an tsaro na dindindin a yankin Alelu–Kimba–Jandutsi, a tallafa wa iyalan da lamarin ya shafa, sannan gwamnan ya kai ziyara domin ganin halin da suke ciki.
Rahoton Daily Post ya bayyana cewa hare-haren sun kawo cikas ga noma, sun lalata gidaje, tare da tilasta wa iyalai da dama barin muhallansu.
Lamarin na faruwa ne a daidai lokacin da ake ƙara samun muhawarar siyasa gabanin zaɓen gwamnan jihar na 2027. Gwamnatin jihar ta zargi jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC) da yaɗa bayanan ƙarya da kuma ɗaukar nauyin rikicin siyasa, zargin da aka ambata a rahoton.
