Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana cewa gwamnatinsa na da cikakken iko kan al’amuran tsaro a jihar, yana mai cewa bai taɓa yin sakaci da alhakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba. Gwamnan ya yi wannan furuci ne yayin da yake jawabi ga mutanen da suka rasa matsugunansu sakamakon hare-haren ’yan bindiga, a […]
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana cewa gwamnatinsa na da cikakken iko kan al’amuran tsaro a jihar, yana mai cewa bai taɓa yin sakaci da alhakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba.
Gwamnan ya yi wannan furuci ne yayin da yake jawabi ga mutanen da suka rasa matsugunansu sakamakon hare-haren ’yan bindiga, a fadar Sarkin Sakaba da ke Dirin-Daji a ƙarshen mako.
Idris ya zargi ’yan siyasar adawa da amfani da matsalar tsaro domin cimma muradun siyasa, yana mai cewa ba su ɗauki matakan magance matsalar ba a lokacin da suke kan mulki, kuma ba su nuna tausayi ko taimaka wa waɗanda hare-haren suka shafa ba.
Ya tabbatar wa mutanen da suka rasa matsugunansu cewa gwamnatinsa za ta mayar da su garuruwa da ƙauyukansu nan ba da jimawa ba domin su ci gaba da harkokin noma.
Gwamnan ya kuma zargi wasu ’yan adawa da amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa bayanan da ya kira ƙarya kan matsalar tsaro, tare da danganta hare-haren da abin da suka bayyana a matsayin gazawar gwamnati.
Ya ce gwamnatinsa ta gaji matsalar tsaro, amma haɗin gwiwa mai ɗorewa tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro ya taimaka wajen inganta yanayin tsaro a jihar.
A cewarsa, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kafa ƙarin rundunonin soji guda uku a Kebbi, tare da ɗaga matsayin Bataliya ta Ɗaya da ke Birnin Kebbi zuwa matakin Birged, da kuma tura ƙarin kayan aikin soji, ciki har da motocin yaƙi masu sulke (APCs) da jami’an rundunar musamman.
