Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi alƙawarin ɗaukar ƙarin matakan tsaro a Ƙaramar Hukumar Sakaba da Masarautar Zuru, biyo bayan hare-haren ’yan bindiga da suka tilasta wa mazauna wasu al’ummomi barin gidajensu.

 

Brinkle FM ta labarto cewa gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai wa mutanen da suka rasa matsugunansu a Sakaba, inda ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ƙarfafa ayyukan tsaro domin ba su damar komawa gidajensu cikin aminci.

 

Brinkle FM ta ƙara da cewa Idris ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ba da umarnin sayo ƙarin kayan aikin tsaro, ciki har da motocin yaƙi masu sulke, domin tura su yankunan da ke fama da matsalolin tsaro.

 

Haka kuma, gwamnan ya ce ana inganta barikin sojoji na Zuru domin ya iya ɗaukar ƙarin jami’an tsaro. Ya ƙara da cewa gwamnati za ta samar wa jami’an tsaron motocin aiki da sauran kayan aikin da za su taimaka wajen ƙarfafa ayyukansu.

 

A cewar gwamnan, gwamnatin jihar za ta ci gaba da haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya da ƙananan hukumomi domin dawo da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

 

Ya jaddada cewa idan taimakon Gwamnatin Tarayya bai wadatar ba, gwamnatinsa za ta shiga tsakani domin tabbatar da tsaron al’umma, ta yadda jama’a za su samu kwanciyar hankali, manoma kuma su koma gonakinsu ba tare da fargaba ba.

 

Brinkle FM ta kuma labarto cewa Idris ya yi alƙawarin ƙara tallafa wa mutanen da suka rasa matsugunansu, yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a yankunan da hare-haren suka shafa.

 

Gwamnan ya buƙaci mazauna yankunan da su ba hukumomin tsaro haɗin kai, su kasance masu bin doka da oda, tare da kauce wa ayyuka ko kalaman da za su iya haifar da fargaba ko kawo cikas ga ayyukan tsaro. Ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da kada su mayar da matsalar tsaro hanyar neman ribar siyasa.

 

A nasa ɓangaren, Sarkin Zuru, Sanusi Mikailu Sami, tare da Shugaban Ƙaramar Hukumar Sakaba, Dauda Muhammad Sakaba, sun yi kira da a haɗa kai domin dawo da zaman lafiya da inganta tsaro a yankin.