Cibiyar ƴanjarida masu binciken ƙwakwaf ta Wole Soyinka, ta naɗa fitaccen ɗan jarida mai ɗaukar hoto,Sani Mohammed Maikatanga, a matsayin ɗaya daga cikin alƙalan da za su tantance Rahotannin Binciken Ƙwaƙwaf, a gasar da take gudanarwa a duk shekara.

 

Wannan ne karo na 21 da ake gudanar da wannan kyauta ta Wole Soyinka da ta ke girmama tare da yaba wa ƴanjaridar Najeriya waɗanda ayyukansu suka nuna ƙwarewa a aikin bincike, jajircewa wajen bin ƙa’ida da kuma nuna bajinta a aikin jaridar da ke kare muradun jama’a.

 

A cikin wasiƙar naɗin da Darakta Janar ta WSCIJ, Motunrayo Alaka, ta sanya wa hannu, an bayyana cewa; ‘A matsayinka na mamba a Kwamitin Alkalai, za ka taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da sahihanci da martabar wannan kyauta, tare da taimakawa wajen gano da karrama fitattun ayyukan bincike da ƴanjaridar a Najeriya suka yi.”

 

Maikatanga ya fara aikinsa na daukar hoto a shekara ta 2000 a matsayin mai ba da rahoto da mai daukar hoto ga mujallar FIM Magazine da ke rawaito wainar da ake toyawa a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

 

Daga baya ya yi aiki a matsayin mai daukar hoto mai zaman kansa na Jaridar Leadership daga 2005 zuwa 2006 kafin ya shiga Media Trust, masu wallafa jaridar Daily Trust, a cikin 2009.

 

Ya samu lambobin yabo da dama ta hanyar ɗaukar hotuna da suka haɗa da fannin Ilimi, al’adu, lafiya, zaman takewa da nishaɗi.