Hukumomin ƙasar Saudiyya sun ce filin jirgin saman ƙasa da ƙasa da ke birnin Riyadh zai ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa aƙalla ranar Asabar, sakamakon hare-haren da ƴan tawayen Houthi na Yemen ke ci gaba da kai wa kan birnin. Da yammacin jiya Litinin, ƙungiyar ta bayyana cewa ta kai hari […]
Hukumomin ƙasar Saudiyya sun ce filin jirgin saman ƙasa da ƙasa da ke birnin Riyadh zai ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa aƙalla ranar Asabar, sakamakon hare-haren da ƴan tawayen Houthi na Yemen ke ci gaba da kai wa kan birnin.
Da yammacin jiya Litinin, ƙungiyar ta bayyana cewa ta kai hari kan filin jirgin saman, yayin da rundunar sojin Saudiyya ta ce ta kakkabo wani makami mai linzami da aka harba zuwa birnin na Riyadh.
Wakiliyar BBC ta ce A Yemen, mayakan Houthi sun tsaurara ƙawanyar da suka yi wa birnin Taiz – wanda ke ƙarkashin ikon gwamnatin da ƙasashen duniya suka amince da ita.
Yaƙin da ke gudana a yankin yana haifar da damuwa game da tasirin da zai yi ga tattalin arzikin duniya.
