Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da take zargi da amfani da yara wajen yin yaƙi ƙarƙashin dokar hana ɗaukar yara aikin soji wato Child Soldiers Prevention Act.

 

Ta yi gargaɗin cewa wannan mataki na iya kai ga Amurkar ta rage bai wa sojojin ƙasar horo, ko sayar mata da makamai, ko bayar da tallafin soji, ko kuma hadin gwiwar tsaro daga ranar 1 ga Oktoba, 2026, sai dai idan Shugaba Donald Trump ya bayar da sassauci.

 

Wannan mataki ya biyo bayan rahoto kan safarar mutane na 2026 da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar, wanda ya zargi kungiyoyin Boko Haram da ISIS reshen Yammacin Afirka da ci gaba da ɗaukar yara aiki tare da amfani da su a rikice-rikice a Najeriya.

 

Rahoton ya sanya Najeriya cikin jerin kasashe 14 da ake zargi da ɗauka ko amfani da yara sojoji, ciki har da Rasha da Iran da Sudan ta Kudu da Somaliya.