Jami’an shige da fice na Amurka sun gudanar da bincike a gidan ‘yar majalisar dokokin Amurka daga jihar Minnesota, Ilhan Omar, a wani ɓangare na binciken aikta laifi da ake yi. Mai magana da yawun Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ya ce jami’an Hukumar Binciken Tsaron Cikin Gida (HSI) sun aiwatar da umurnin yin bincike […]
Jami’an shige da fice na Amurka sun gudanar da bincike a gidan ‘yar majalisar dokokin Amurka daga jihar Minnesota, Ilhan Omar, a wani ɓangare na binciken aikta laifi da ake yi.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ya ce jami’an Hukumar Binciken Tsaron Cikin Gida (HSI) sun aiwatar da umurnin yin bincike ne da wata kotu ta amince da shi a wani gida da ke yankin Washington DC.
Sai dai bai yi ƙarin bayani kan binciken ba.
Haka kuma babu tabbacin ko Omar tana gida a lokacin da aka gudanar da binciken, saboda majalisar dokokin Amurka na hutu a halin yanzu.
Omar, wadda ‘yar jam’iyyar Democrat ce kuma mai yawan sukar Shugaba Donald Trump, ta wallafa a shafukanta na sada zumunta cewa matakin wani yunƙuri ne na “musgunawa abokan hamayya na siyasa da kuma amfani da jami’ian gwamnati a matsayin makamin siyasa.”
Da yake magana da manema labarai, Shugaba Trump ya ce ba shi da wata alaƙa da binciken da ma’aikatar shari’a ke yi wa Omar.”
