Daga Sashen Labarai na Brinkle FM
Majalisar Yakin Neman Zaben Tinubu/Dikko 2027 a Jihar Katsina ta nada fitaccen dan jarida, Alhaji Muhammed Lawal Maikudi, a matsayin mamba a Sashen Yada Labarai da Hulda da Jama’a, gabanin babban zaben shekarar 2027.
Maikudi gogaggen dan jarida ne kuma mawallafin jaridar intanet ta Kunnen Gari, mai hedikwata a Kaduna.
Nadin nasa na kunshe ne cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 14 ga Oktoba, 2026, wadda Darakta Janar na Majalisar Yakin Neman Zaben, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, FNIA, ya sanya wa hannu a madadin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda.
A cewar wasikar, an nada Maikudi ne bisa la’akari da kwarewarsa, jajircewarsa da kuma cancantarsa wajen bayar da gudunmawa mai ma’ana domin cimma manufofin Majalisar.
Majalisar ta bayyana cewa Sashen Yada Labarai da Hulda da Jama’a zai taka muhimmiyar rawa wajen tsarawa, hada kai da aiwatar da ayyukan yakin neman zabe, tare da yin aiki kafada da kafada da sauran sassa da masu ruwa da tsaki.
Ta kuma bukaci Maikudi da ya gudanar da ayyukan da aka dora masa cikin gaskiya, rikon amana, ladabi da kishin aiki, tare da karfafa hadin kai domin cimma muradun Majalisar.
Haka kuma, wasikar ta bukaci sabon mamban da ya tabbatar da amincewarsa da nadin a rubuce cikin sa’o’i 48 bayan karbar wasikar.
A ranar Litinin, 19 ga Oktoba, 2026, aka gudanar da bikin kaddamar da Majalisar a ofishinta da ke kan titin Kano Expressway, Dandagoro, a birnin Katsina.
Nadin Maikudi na daga cikin matakan da Majalisar ke dauka domin karfafa tsarinta da shirye-shiryenta gabanin babban zaben shekarar 2027, yayin da harkokin siyasa ke kara daukar zafi a sassan Najeriya.
Brinkle FM ta rawaito cewa Darakta Janar na Majalisar Yakin Neman Zaben Tinubu/Dikko 2027, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ne ya sanya hannu kan wasikar nadin.