Daga Wakilinmu Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, kuma jigo a jam’iyyar ADC, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya ƙaryata soki-burutsun da ake cewa ya sauya sheƙa daga ADC. Tambuwal wanda ya yi gwamna a Jihar Sokoto tsawon shekaru takwas, yanzu kuma yake Majalisar Dattawa, ya ƙaryata wannan jita-jitar a cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa […]
Daga Wakilinmu
Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, kuma jigo a jam’iyyar ADC, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya ƙaryata soki-burutsun da ake cewa ya sauya sheƙa daga ADC.
Tambuwal wanda ya yi gwamna a Jihar Sokoto tsawon shekaru takwas, yanzu kuma yake Majalisar Dattawa, ya ƙaryata wannan jita-jitar a cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran sa mai suna Prince Daniel ya raba wa manema labarai a ranar Litinin.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Daniel, ya ce a yi watsi da iƙirarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta da ke nuna cewa Sanata Aminu Waziri Tambuwal na shirin ficewa daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
“Muna bayyanawa ƙarara cewa Sanata Tambuwal ba shi da wani shirin komawa APC. Duk wani iƙirarin da ke nuna akasin haka ƙarya ce, ba ta da tushe, kuma bai kamata a ɗauke ta da muhimmanci ba.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa Sanata Tambuwal gogaggen ɗan siyasa ne kuma fitaccen ɗan ƙasa wanda ya daɗe yana da kyakkyawar alaƙa da abokai a faɗin jam’iyyun siyasa daban-daban.
“Waɗannan alaƙoƙi sun samo asali ne daga shekarun hidimar jama’a da mutunta juna. Bai kamata a karkatar da ma’anar irin waɗannan alaƙoƙi ko a fassara su a matsayin alamar sauya sheƙar siyasa ba.”
Ya ce hotuna da gajerun bidiyoyin da ake yaɗawa ba su zama hujjar cewa Sanata Tambuwal na shirin sauya sheƙa ba. Mu’amala cikin mutunci tsakanin ’yan siyasa ba ta nufin sauya sheƙa. Haka kuma, gaisawa ko tattaunawa da ’yan wata jam’iyya ba ya tabbatar da cewa ana shirin sauya sheƙa.” Cewar sanarwar.
“Sanata Tambuwal yana nan daram a jam’iyyar ADC, kuma ya himmatu wajen ƙarfafa jam’iyyar, faɗaɗa haɗin gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki, tare da tattara goyon bayan ’yan Nijeriya gabanin babban zaɓen shekarar 2027.”
Ya ce a daidai lokacin da ’yan Nijeriya ke buƙatar sahihan amsoshi kan ƙalubalen tattalin arziki, tsaro da shugabanci, ya kamata muhawarar jama’a ta mayar da hankali kan muhimman batutuwa da sahihan bayanai. Bai kamata hasashe marasa tushe su karkatar da hankalin jama’a daga muhimmin aikin samar da shugabanci nagari da kyakkyawar makoma ga ’yan Nijeriya ba.
“Muna kira ga magoya baya da sauran jama’a da su ci gaba da mai da hankali kan ayyukan da ke gabanmu. Ƙudurin Sanata Tambuwal na tabbatar da shugabanci na gari, riƙon amana, mutunta ƙa’idojin dimokraɗiyya da inganta walwalar ’yan Nijeriya bai sauya ba.
Haka kuma, muna kira ga kafafen yaɗa labarai da masu sharhi a kafafen sada zumunta da su tabbatar da sahihancin duk wani bayani ta hanyar tuntuɓar Ofishin Yaɗa Labarai na Aminu Waziri Tambuwal (AWT) kafin wallafa shi.
“Bai kamata a gabatar da jita-jita ko hasashe a matsayin tabbatacciyar gaskiya ba.” Inji Tambuwal.
