• Daga GARBA MUHAMMAD

 

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) da gwamnatin ƙasar Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2027, tare da sabunta aniyar inganta ayyukan Hajji da tabbatar da jin daɗi, tsaro da walwalar alhazan Najeriya.

 

An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamba, 2026, a cibiyar Super Dome da ke birnin Jeddah na ƙasar Saudiyya.

 

Shugaban Hukumar NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ne ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da Mataimakin Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dakta Abdulfattah bin Sulaiman Mashat, ya sanya hannu a madadin gwamnatin Saudiyya.

 

Yarjejeniyar ta ƙunshi muhimman batutuwan da suka shafi gudanar da aikin Hajji, ciki har da adadin kujerun alhazan Najeriya, masauki, sufuri, kiwon lafiya, bin dokokin Saudiyya da kuma kiyaye wa’adin shirye-shiryen Hajji.

 

Da yake jawabi a wajen bikin, Ambasada Ismail Abba Yusuf ya yaba wa gwamnatin Saudiyya bisa ci gaba da zuba jari wajen inganta kayayyakin more rayuwa da ayyukan da suka shafi Hajji.

 

Ya tabbatar da cewa hukumar NAHCON za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin Saudiyya domin samar da ingantattun ayyuka da sauƙaƙa wa alhazan Najeriya gudanar da ibadarsu cikin kwanciyar hankali.

 

A nasa jawabin, Mataimakin Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dakta Mashat, ya bayyana cewa ƙasar ta samu gamsuwar alhazai da ayyukan Hajjin 2026 da kaso 93 cikin 100.

 

Ya yaba wa Najeriya bisa gudunmawar da ta bayar wajen cimma wannan nasara, musamman yadda hukumar NAHCON ta cika dukkan wa’adin da aka shimfiɗa mata na shirye-shiryen Hajjin 2027.

 

Dakta Mashat ya buƙaci Najeriya ta ci gaba da kiyaye wannan nasara ta hanyar kyakkyawan shiri, haɗin kai da bin ƙa’idojin gudanar da aikin Hajji na Saudiyya.

 

Taron rattaba hannu kan yarjejeniyar ya samu halartar Jakadan Najeriya a Saudiyya, Ambasada Yakubu Gambo, da tawagar ‘yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kwamitin Hajji na Majalisar Wakilai, Hon. Jafar Mohammed, tare da wasu manyan jami’an gwamnati.

 

A halin da ake ciki, hukumar NAHCON ta bayyana cewa za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, kamfanonin yawon buɗe ido masu lasisi da hukumomin Saudiyya domin magance matsalolin da ka iya tasowa kafin fara aikin Hajjin 2027.

 

Hukumar ta ce haɗin gwiwar zai mayar da hankali kan inganta ayyukan Hajji, sa ido kan ingancin hidimomi da kuma kare haƙƙoƙi da jin daɗin alhazan Najeriya.

 

Wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Wallafe-wallafe na NAHCON, Shafii Sani Mohammed, ya fitar ta bayyana yarjejeniyar a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin tsari da nasara.

 

Gidan Rediyon Brinkle FM 93.9 Zuru ya rawaito cewa ana sa ran wannan yarjejeniya za ta taimaka wajen inganta shirye-shiryen Hajjin 2027, musamman a fannonin masauki, sufuri, kiwon lafiya da kuma walwalar alhazan Najeriya.