Daga GARBA DANJARIDA

 

Shugaban Ƙungiyar Jama’atul Izalatul Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) na Ƙasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya musanta zarge-zargen da ke yawo a shafukan sada zumunta cewa ya karɓi maƙudan kuɗaɗe domin yi wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kamfen na sake zaɓensa a shekarar 2027.

 

Sheikh Jingir ya bayyana zarge-zargen a matsayin marasa tushe, yana mai jaddada cewa goyon bayan da yake bai wa gwamnatin Tinubu ya samo asali ne daga fahimtarsa ta addinin Musulunci, ba wai saboda an ba shi kuɗi ko kasancewarsa ɗan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ba.

 

Malamin addinin Musuluncin ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga mambobin ƙungiyar a taron shiyyar Arewa maso Yamma da babban taron ƙarawa juna sani na ƙasa, wanda aka gudanar a hedikwatar Jama’atu Nasril Islam (JNI) da ke Kaduna.

 

Ya bayyana cewa duk da cewa shi ba ɗan jam’iyyar APC ba ne, ya goyi bayan takarar Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, waɗanda dukkaninsu Musulmai ne, a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.

 

A cewarsa, matsayarsa kan tikitin takarar Musulmi da Musulmi ya samo asali ne daga fahimtarsa game da koyarwar addinin Musulunci, musamman hujjoji daga Alƙur’ani Mai Girma da Hadisan Manzon Allah (SAW), ba wai saboda son zuciya ko wata manufa ta siyasa ba.

 

Sheikh Jingir ya ƙara da cewa duk wata shawara ko jagoranci da yake bayarwa kan harkokin addini da siyasa yana dogara ne da hujjoji da ƙa’idojin Musulunci, yana mai jaddada cewa ba ya tilasta wa mabiyansa bin ra’ayinsa na kashin kai.

 

Da yake jawabi a wajen taron, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu Shawara kan Harkokin Siyasa, Hon. Kabiru Masari, wanda mataimakinsa na musamman, Alhaji Sabiu Saidu Mahuta, ya wakilta, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu a shekarar 2027.

 

Masari ya bayyana cewa bai wa Tinubu damar kammala wa’adin mulki na shekaru takwas zai taimaka wajen ɗorewar sauye-sauye, tsare-tsare da shirye-shiryen gwamnatinsa domin inganta tattalin arziki da walwalar al’ummar Najeriya.

 

Ya kuma nuna kyakkyawan fata cewa ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi na magance matsalar tsaro, musamman a yankin Arewa maso Yamma, yana fara haifar da sakamako mai kyau.

 

A cewarsa, gwamnatin Tinubu na ci gaba da jajircewa wajen yaƙi da ta’addanci, talauci, jahilci da matsalolin tattalin arziki da ke addabar ‘yan Najeriya.

 

Ya ce, “Da ƙuduri da jajircewar Shugaba Tinubu, muna da yaƙinin cewa, da yardar Allah, matsalolin rashin tsaro, talauci, jahilci da tsadar rayuwa za su zama tarihi.”

 

Shi ma da yake jawabi, Shugaban Majalisar Malamai ta JIBWIS a Jihar Legas, Sheikh Dalhatu Abubakar Abdullahi Santana, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin wayar da kan mambobin ƙungiyar game da shiga harkokin siyasa bisa mahangar addinin Musulunci.

 

Ya bayyana cewa taron na da manufar ƙarfafa al’umma su shiga harkokin siyasa cikin sanin ya kamata, tare da fahimtar haƙƙoƙinsu da nauyin da ya rataya a wuyansu a tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya, musamman yayin da ake tunkarar wani sabon zagayen zaɓe.

 

Sheikh Santana ya jaddada cewa bai kamata a ɗauki ra’ayoyin Sheikh Jingir kan harkokin siyasa a matsayin nuna goyon baya ga wata jam’iyya kaɗai ko kuma kasancewarsa memba na wata jam’iyyar siyasa ba.

 

Ya ce malamin ya daɗe yana bai wa ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban shawarwari bisa koyarwar addinin Musulunci da tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

 

A cewar Santana, kowane ɗan Najeriya, ba tare da la’akari da addininsa ba, yana da ‘yancin faɗar albarkacin bakinsa, shiga ƙungiyoyi da kuma gudanar da harkokin siyasa kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin ƙasa ya tanada.

 

Ya yi kira ga Musulmai da su riƙa yanke shawara kan harkokin siyasa bisa sahihan hujjoji, kyakkyawan tunani da koyarwar addinin Musulunci, maimakon bin son zuciya, biyayya ta makauniya ko yaɗa bayanan ƙarya.

 

Malamin ya ƙara jaddada cewa ƙungiyar JIBWIS za ta ci gaba da ƙarfafa fahimtar addini, zaman lafiya, haɗin kan al’umma da shiga harkokin siyasa cikin sanin ya kamata, ba tare da yin watsi da ƙa’idoji da manufofin addinin Musulunci ba.