Daga Garba Danjarida Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana cewa jihar ta zo ta biyar a duk faɗin Najeriya, yayin da ta zama ta farko a jihohi 19 na Arewacin Najeriya wajen ingantaccen tsarin gudanar da kuɗaɗen gwamnati, kamar yadda rahoton BudgIT na shekarar 2026 ya nuna. Kwamishinan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki […]
Daga Garba Danjarida
Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana cewa jihar ta zo ta biyar a duk faɗin Najeriya, yayin da ta zama ta farko a jihohi 19 na Arewacin Najeriya wajen ingantaccen tsarin gudanar da kuɗaɗen gwamnati, kamar yadda rahoton BudgIT na shekarar 2026 ya nuna.
Kwamishinan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki na jihar, Dakta Abba Sani Kalgo, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Asabar a Birnin Kebbi.
Kwamishinan ya ce wannan nasara ta nuna irin ƙoƙarin gwamnatin Gwamna Kwamared Dakta Nasir Idris, Kauran Gwandu, wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma amfani da dukiyar al’umma yadda ya kamata.
A cewarsa, rahoton BudgIT, wanda ya tantance yadda jihohi 36 na Najeriya suka gudanar da harkokin kuɗaɗensu a shekarar 2025, ya sanya Kebbi a matsayi na farko a Arewa da na biyar a Najeriya.
Ya bayyana cewa an yi wannan tantancewa ne bisa la’akari da yadda jihohi ke samun kuɗaɗen shiga, sarrafa basussuka, gudanar da kasafin kuɗi da kuma zuba jari a muhimman fannoni kamar noma, ilimi, lafiya, ruwa da tsaftar muhalli.
Dakta Kalgo ya ce jimillar kuɗaɗen shigar Jihar Kebbi ta ƙaru da kashi 59.54 cikin ɗari a shekarar 2025, yayin da kuɗaɗen shiga da jihar ke samarwa da kanta suka ƙaru da kashi 107.81 cikin ɗari, inda suka kai naira biliyan 23.62.
Haka kuma, ya bayyana cewa jihar ta samu rarar kuɗi na naira biliyan 15.13, mafi girma a yankin Arewa maso Yamma, yayin da kuɗaɗen da aka kashe wajen ayyukan raya ƙasa suka ƙaru da kashi 60.08 cikin ɗari, wanda ya kai kashi 63.45 na jimillar kuɗaɗen da gwamnati ta kashe.
Dangane da basussuka kuwa, Kwamishinan ya ce kuɗaɗen da jihar ke kashewa wajen biyan basussuka sun kai kashi 2.40 cikin ɗari kacal na jimillar kuɗaɗen shigarta, lamarin da ya sanya Kebbi a matsayi na huɗu cikin jihohin da ke da ƙarancin basussuka a Najeriya.
Ya danganta wannan ci gaba da sauye-sauyen da gwamnatin Nasir Idris ta aiwatar wajen inganta tara kuɗaɗen shiga, tabbatar da gaskiya a kasafin kuɗi da kuma rage almubazzaranci da dukiyar gwamnati.
Da yake mayar da martani kan zarge-zargen rashin iya tafiyar da kuɗaɗen jihar da jam’iyyar ADC ta yi, Dakta Kalgo ya ce rahoton BudgIT ya samar da hujjoji masu zaman kansu da za a iya amfani da su wajen tantance yadda gwamnatin ke gudanar da harkokin kuɗaɗenta.
Ya ƙalubalanci jam’iyyar adawar da ta nazarci rahoton tare da gabatar da suka mai ma’ana bisa sahihan bayanai, maimakon zarge-zargen siyasa.
Kwamishinan ya tabbatar wa al’ummar Kebbi cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da inganta hanyoyin samun kuɗaɗen shiga tare da kammala ayyukan raya ƙasa da ake gudanarwa a ƙananan hukumomi 21 na jihar.
Ya ce gwamnatin za ta ci gaba da ba da fifiko ga gina hanyoyi, makarantu, asibitoci, samar da ruwan sha da tallafa wa manoma domin inganta rayuwar al’umma.
Taron manema labaran ya samu halartar Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Yakubu Ahmed-BK, tare da masu taimaka wa Gwamna Nasir Idris kan harkokin yaɗa labarai.
Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Gwamnan Kebbi Shawara ta Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Yahaya Sarki, ya fitar ranar Asabar, 7 ga Nuwamba, 2026.
