Al-Amin Musa, Zuru

 

Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana cewa rashin biyan tsohon Gwamnan jihar na farko, Alhaji Abubakar Musa Garkuwan Yauri, kudaden fansho da garatuti ya samo asali ne daga tanade-tanaden doka, ba wai saboda bambancin siyasa ba.

 

Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Birnin Kebbi ranar Talata.

 

Ya ce Garkuwan Yauri ya yi mulki daga Janairun 1992 zuwa Nuwamban 1993, na tsawon watanni 22, wanda a fassarar gwamnatin bai kai shekaru biyu da ake bukata domin samun wasu kudaden sallamar tsofaffin gwamnoni ba.

 

Kwamishinan ya ce matsayar gwamnatin ta dogara ne kan Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 da Dokar Fansho da Garatuti ta Tsofaffin Gwamnonin Kebbi ta shekarar 2004.

 

Ya kuma musanta zargin cewa Gwamna Nasir Idris ya yi watsi da Garkuwan Yauri.

 

A cewarsa, gwamnatin ta ba tsohon Gwamnan tallafin kudi da kayayyaki, tare da daukar nauyin tafiye-tafiyensa zuwa kasar Masar domin neman lafiya fiye da sau biyu.

 

Ya kara da cewa gwamnatin ta sanya sunansa a wani dakin taro na Fadar Gwamnati, tare da taimaka wa dansa wajen samun mukamin jakada.

 

Kwamishinan ya bukaci Garkuwan Yauri da ya yaba wa ayyukan raya kasa da gwamnatin Nasir Idris ke gudanarwa, musamman a garin Warah.

 

Ya jaddada cewa Gwamna Nasir Idris na mutunta tsohon Gwamnan, kuma bambancin siyasa ba zai hana gwamnatin ci gaba da kyautata alaka da dattawan jihar ba.

 

Sanarwar ta fito ne daga Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Yada Labarai, Yahaya Sarki, a ranar 20 ga Oktoba, 2026.