Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matsalar tsaro da korar al’umma daga muhallansu a Jihar Kebbi a matsayin gaggawar tsaron ƙasa da ta jin ƙai. Ƙudirin da Sanata Adamu Aliero ya gabatar ya biyo bayan hare-haren ’yan bindiga da suka haddasa asarar rayuka, tare da tilasta wa mazauna yankunan barin […]
Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matsalar tsaro da korar al’umma daga muhallansu a Jihar Kebbi a matsayin gaggawar tsaron ƙasa da ta jin ƙai.
Ƙudirin da Sanata Adamu Aliero ya gabatar ya biyo bayan hare-haren ’yan bindiga da suka haddasa asarar rayuka, tare da tilasta wa mazauna yankunan barin gidajensu da hanyoyin neman abincinsu.
Majalisar ta bukaci a tura ƙarin jami’an tsaro da kayan aiki, tare da ƙarfafa haɗin gwiwar rundunonin soji da ’yan sanda wajen dakile hare-haren.
Haka kuma, ta umarci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da ta samar wa waɗanda suka rasa matsugunansu da abinci, ruwa, matsuguni, tufafi, magunguna da sauran kayan agaji.
Majalisar ta kuma bukaci Gwamnatocin Tarayya da na Jihar Kebbi su haɗa kai wajen magance matsalar, tabbatar da dawowar mutanen da suka tsere cikin aminci, da gyara kayayyakin more rayuwa da suka lalace.
Bugu da ƙari, ta nemi gudanar da cikakken bincike kan kashe-kashen da aka yi, ciki har da mutuwar ma’aikata uku na kamfanin Hitech.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya jajanta wa al’ummomin da abin ya shafa, tare da bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kuduri aniyar dawo da zaman lafiya da taimaka wa waɗanda suka rasa matsugunansu.
