Sanata Muhammad Adamu Aliero ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakan tsaro da agajin jin ƙai, biyo bayan tilasta wa mazauna wasu yankunan ƙananan hukumomin Jega da Maiyama na Jihar Kebbi barin gidajensu sakamakon hare-haren ’yan bindiga.

 

Sanatan, wanda ke wakiltar mazabar Kebbi ta Tsakiya, ya yi wannan kira ne a cikin wani ƙudiri kan batun da ke buƙatar kulawar gaggawa ta ƙasa, wanda ya gabatar a gaban Majalisar Dattawa.

 

Aliero ya bayyana cewa ana zargin wasu ’yan bindiga da tserewa zuwa wasu al’ummomin Kebbi bayan tsananta hare-haren sojoji a jihohin Zamfara da Sokoto, lamarin da ya haifar da sabbin barazanar tsaro tare da tilasta wa mazauna yankunan tserewa daga gidajensu.

 

A cewar ƙudirin, yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Jan Dutsi, Agada, Kimba, Alelu, Tanja, Jadadi, Bawanka, Kaba, Zugu, Tafkin Kada da Gehuru.

 

Sanatan ya ce hare-haren sun jefa mazauna yankunan cikin fargaba da barazana, tare da haddasa lalacewar dukiyoyi da asarar rayuka. Hakan ya tilasta wa mutane da dama neman mafaka a garuruwan Jega, Aliero da Maiyama, waɗanda su ne hedikwatocin ƙananan hukumomin da abin ya shafa.

 

Ya kuma nuna damuwa kan rahotannin kashe ma’aikata uku na kamfanin Hi-Tech, wanda ke gudanar da aikin babbar hanyar Badagry–Sokoto Superhighway, a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara.

 

Aliero ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kebbi bisa taimakon da ta samar wa waɗanda suka rasa matsugunansu, ciki har da matsuguni da abinci da sauran tallafi. Sai dai ya jaddada cewa girman matsalar jin ƙai da ta kunno kai na buƙatar ƙarin tallafi daga Gwamnatin Tarayya.

 

Sanatan ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta samar wa hukumomin tsaro isassun jami’ai, kayan aiki da tallafin sufuri da sauran dabaru domin dakile hare-haren tare da dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

 

Haka kuma, ƙudirin ya yi kira ga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da ta tantance buƙatun mutanen da suka rasa matsugunansu, tare da samar musu da abinci, ruwa, matsuguni na wucin gadi, magunguna da sauran kayayyakin agaji.

 

Aliero ya kuma bukaci gwamnatocin tarayya da na jiha su haɗa kai wajen aiwatar da matakan tsaro da agajin jin ƙai, tare da tabbatar da cewa mutanen da suka tsere za su iya komawa gidajensu cikin aminci da zarar an tabbatar da tsaron yankunansu.