Daga Garba Muhammad | Brinkle FM 93.9 Zuru

 

Manoma daga kananan hukumomi 21 na Jihar Kebbi sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Gwamna Nasir Idris, Kauran Gwandu, domin sake zabensa a babban zaben shekarar 2027.

 

Manoman, karkashin kungiyar Equity Farmers Association, sun bayyana wannan matsaya ne a ranar Alhamis, yayin wani gagarumin taro da suka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar Kebbi da ke Birnin Kebbi.

 

Da yake jawabi a madadin manoman, Shugaban kungiyar, Alhaji Abubakar Goje, ya bayyana cewa sun yanke shawarar marawa Gwamna Nasir Idris baya ne saboda irin gudunmawar da gwamnatinsa ke bayarwa wajen bunkasa harkokin noma da inganta rayuwar manoma a jihar.

 

Alhaji Abubakar Goje ya ce kungiyar ta kunshi kungiyoyin manoma daban-daban daga kananan hukumomi 21 na jihar, wadanda suka kuduri aniyar hada kai domin tabbatar da nasarar gwamnan a zaben 2027.

 

Ya bayyana cewa tallafin kayan aikin noma, iri da sauran kayayyakin bunkasa noma da gwamnatin ke bayarwa sun kara karfafa amincewar manoma ga shugabancin Kauran Gwandu.

 

A cewarsa, manoman sun shirya tsaf domin wayar da kan jama’a da kuma gangamin neman goyon bayan gwamnan tun daga matakin unguwanni har zuwa kananan hukumomi.

 

Alhaji Goje ya ce, “Mu manoma mun amince da kai. Mun dauki alkawarin mara maka baya, kuma a shirye muke mu hada kan mambobinmu a fadin jihar domin tabbatar da nasararka a zabe.”

 

A nata jawabin, Shugabar Mata ta kungiyar, Hajiya Raliya Abubakar Yer Buga Unity, ta tabbatar da cewa mata manoma da sauran kungiyoyin mata a jihar za su bayar da cikakken goyon baya ga kudirin sake zaben Gwamna Nasir Idris.

 

Ta ce mata za su gudanar da gangamin gida-gida domin fadakar da jama’a kan ayyukan ci gaba da gwamnatin ke aiwatarwa, tare da neman goyon baya ga gwamnan.

 

Hajiya Raliya ta kuma yaba wa gwamnatin jihar bisa ayyukan raya kasa da take gudanarwa a kananan hukumomi daban-daban.

 

Shi ma da yake magana, Mai Baiwa Gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa da Mulki, Alhaji Kabiru Sani Giant, ya bayyana taron a matsayin wata babbar alama ta amincewar manoma da shugabancin Gwamna Nasir Idris.

 

Ya yaba wa manoman bisa gabatar da kayayyakin amfanin gona da suka hada da albasa, dankalin Turawa, shinkafa da wake, a matsayin kyautar nuna godiya da goyon baya ga gwamnan.

 

Alhaji Kabiru Sani Giant ya kuma yi kira ga dukkan wadanda suka cancanci kada kuri’a da su tabbatar sun mallaki katin zabe na dindindin, wato PVC, domin samun damar shiga zaben shekarar 2027.

 

Da yake mayar da martani, Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, Kauran Gwandu, ya gode wa Allah Madaukakin Sarki da kuma manoman bisa irin wannan gagarumin goyon baya da suka nuna masa.

 

Gwamnan ya bayyana cewa wannan goyon baya wata shaida ce ta yadda manufofi da shirye-shiryen gwamnatinsa ke amfani ga al’ummar jihar, musamman manoma.

 

Ya ce Jihar Kebbi na ci gaba da kasancewa daya daga cikin manyan jihohin da ke samar da abinci a Najeriya, yana mai tabbatar da cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tallafa wa manoma.

 

Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa gwamnatinsa ta raba kayayyakin aikin noma da suka hada da injinan ban-ruwa masu amfani da hasken rana, injinan dizal, injinan nome kasa, injinan girbin amfanin gona da sauran kayan aikin noma na zamani.

 

Ya kuma tabbatar wa manoma da kungiyoyin da ba su samu tallafi ba cewa za a yi la’akari da su a shirye-shiryen rabon tallafi na gaba.

 

A yayin taron, Gwamna Nasir Idris ya sanar da bayar da tallafin Naira miliyan 50 ga kungiyar Equity Farmers Association, domin nuna godiya bisa goyon bayan da ta bayyana masa.

 

Gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah Ya ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaba a Jihar Kebbi.

 

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Baiwa Gwamnan Jihar Kebbi Shawara na Musamman kan Yada Labarai, Yahaya Sarki, ya fitar, wadda aka aikewa Brinkle FM.

 

Brinkle FM 93.9 Zuru — Fiye da Rediyo, Muna Hada Ku da Duniya.