…Ta yi maraba da sakinta kan beli, tana jiran sake sauraron shari’a ranar 3 ga Nuwamba

 

Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) ta bukaci a yi adalci ga Farida Isiak, ‘yar jarida mai shekaru 23 da ke aiki da Rediyon Nagarta a Kaduna, wadda aka ruwaito cewa an yanke mata hukuncin daurin shekaru hudu ko tarar Naira miliyan 1.75 saboda wani rubutu a Facebook.

 

Lamarin ya samo asali ne daga takaddama kan canjin Naira 100 na cinikin gawayi tsakanin mahaifiyar Farida da wata makwabciya.

 

An ruwaito cewa ‘yan sanda sun kama mahaifiyarta, sannan suka tsare mahaifinta lokacin da ya je neman belinta.

 

Farida ta wallafa rubutu tana sukar matakin ‘yan sandan, lamarin da ya kai ga zarginta da bata sunan rundunar.

 

A cewar NUJ, duk da cewa ta goge rubutun tare da bayar da hakuri, an gurfanar da ita a wata kotu da ke Kawo, inda aka ruwaito cewa aka yanke mata hukuncin.

 

Sai dai lauyoyi sun shiga tsakani kafin a kai ta gidan gyaran hali, daga bisani kuma aka bayar da belinta.

 

An shirya sake sauraron shari’ar ranar 3 ga Nuwamba, 2026, amma har yanzu ba a fayyace ko an soke hukuncin farko a hukumance ba.

 

A sanarwar da Shugaban NUJ na Kasa, Alhassan Yahya Abdullahi, ya sanya wa hannu ranar Alhamis, 22 ga Oktoba, kungiyar ta bukaci a binciki yadda aka kama Farida da iyayenta.

 

Ta kuma bukaci hukumomin shari’a su tabbatar da adalci, tare da nazarin hurumin kotun da kuma dalilan hukuncin da aka ruwaito.

 

NUJ ta ce sukar jami’an gwamnati ba kamata ya zama hanyar tsoratar da jama’a ko tauye musu ‘yancin fadin albarkacin baki ba.

 

Kungiyar ta jaddada cewa sashe na 35, 36 da 39 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya sun kare ‘yancin mutum, damar samun adalci da ‘yancin bayyana ra’ayi.

 

Abdullahi ya ce kare Farida ba wai kare ‘yar jarida daya kawai ba ne, illa kare hakkokin dukkan ‘yan Najeriya.

 

NUJ ta yi alkawarin ci gaba da sa ido kan shari’ar domin tabbatar da adalci da kare ‘yancin aikin jarida.