Daga Asile Abel, Jos

 

Jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, a Jihar Filato, ta gabatar da Hon. Chundung Kele a matsayin mataimakiyar dan takararta na gwamna a zaben shekarar 2027, Birgediya Janar Johnson Sunday Sura mai ritaya.

 

An gudanar da bikin gabatarwar ne ranar Litinin a Cibiyar Taro ta Zumji da ke Jos, inda shugabanni da magoya bayan jam’iyyar daga kananan hukumomi 17 na jihar suka halarta.

 

Da yake jawabi, Sura ya yi alkawarin magance matsalar tsaro, bunkasa tattalin arziki da kuma dawo da martabar Filato a matsayin jihar zaman lafiya da yawon bude ido.

 

Ya ce gwamnatinsa, idan aka zabe shi, za ta mayar da hankali kan inganta tsaro a matakin al’umma, farfado da harkokin noma da kuma jawo masu zuba jari.

 

Sura ya bayyana Kele a matsayin gogaggiyar ‘yar siyasa mai kusanci da jama’a, wadda kwarewarta a harkokin gwamnati za ta taimaka wajen cimma manufofinsu.

 

A nata jawabin, Kele ta yi alkawarin karfafa mata ta fuskar tattalin arziki, tabbatar da shugabanci na kowa da kowa da kuma samar da karin damar dogaro da kai ga al’ummar Filato.

 

Tun da farko, Shugaban ADC na Jihar Filato, Hon. Dung Daweng Pam, ya bukaci magoya bayan jam’iyyar da su kara kaimi wajen neman goyon bayan jama’a gabanin babban zaben 2027.

 

Pam ya kuma soki gwamnatin jam’iyyar APC kan matsalolin tsaro da tsadar rayuwa da ke addabar ‘yan Najeriya.

 

Kele, wadda ta taba zama kansila a Karamar Hukumar Jos ta Kudu, ta kuma rike mukamai a Fadar Gwamnatin Filato da kuma jam’iyyar PDP.

 

Tana da digiri a Kimiyyar Siyasa da kuma digiri na biyu a Harkokin Kasashen Duniya, yayin da take karatun digiri na uku a Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi.

 

Bikin gabatarwar na daga cikin shirye-shiryen jam’iyyar ADC domin tunkarar babban zaben shekarar 2027.

 

Daga Sashen Labarai na Brinkle FM Zuru.