Daga GARBA MUHAMMAD

 

Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana cewa ta kammala shirye-shiryen tarbar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, cikin gagarumin biki a ziyarar da yake shirin kaiwa jihar domin halartar babban taron gangamin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

 

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Kebbi, Hon. Yakubu Ahmed-BK, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Birnin Kebbi, ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba, 2026.

 

Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir Idris, Kauran Gwandu, ya kafa kwamitoci daban-daban domin tsara yadda za a tarbi Shugaban Ƙasa da tawagarsa, tare da tabbatar da gudanar da taron cikin nasara da kwanciyar hankali.

 

A cewarsa, shugabannin jam’iyyar APC, ƙungiyoyin magoya baya da sauran masu ruwa da tsaki sun dukufa wajen wayar da kan jama’a da tattara magoya baya daga ƙananan hukumomi 21 na jihar domin halartar taron.

 

Yakubu Ahmed-BK ya bayyana cewa ziyarar Shugaba Tinubu ba taron siyasa kawai ba ne, illa wata dama ce ga al’ummar Kebbi su nuna goyon bayansu ga shugaban ƙasar da kuma manufofin gwamnatinsa na Renewed Hope Agenda.

 

Ya ce gwamnatin jihar, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris, ta shirya tsaf domin ganin an yi wa Shugaban Ƙasa tarba ta musamman wadda za ta shiga tarihi.

 

Kwamishinan ya ƙara da cewa irin yadda shugabannin siyasa, mata, matasa, manoma, ƙungiyoyin ma’aikata da sauran magoya bayan APC ke nuna sha’awar halartar taron, alama ce da ke nuna irin gagarumar tarbar da Shugaba Tinubu zai samu.

 

Da yake magana kan ayyukan raya ƙasa, Ahmed-BK ya yaba da shirye-shiryen gwamnatin tarayya, musamman aikin babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry, wanda ya ce zai taimaka wajen bunƙasa harkokin sufuri, kasuwanci da tattalin arzikin ƙasa.

 

Ya bayyana cewa Jihar Kebbi, kasancewarta jiha mai dogaro da noma, za ta amfana sosai daga ingantattun hanyoyi wajen jigilar amfanin gona zuwa kasuwanni.

 

Haka kuma, ya ambaci hanyoyin Bachaka da Malando zuwa Ngaski da sauran ayyukan more rayuwa a matsayin muhimman ayyukan da za su taimaka wajen haɗa al’ummomin karkara da bunƙasa tattalin arziki.

 

A fannin siyasa kuwa, Kwamishinan ya sake jaddada cikakken goyon bayan Gwamna Nasir Idris ga takarar Shugaba Tinubu ta neman wa’adi na biyu a zaɓen 2027.

 

Ya tunatar da cewa Kebbi na daga cikin jihohin farko da suka fito fili suka bayyana goyon bayansu ga sake zaɓen Shugaban Ƙasa, yana mai cewa hakan na nuna amincewa da jagorancinsa da kuma buƙatar ci gaba da ayyukan da gwamnatinsa ta fara.

 

Ahmed-BK ya kuma bayyana cewa ƙaruwar farin jinin APC a Jihar Kebbi na da alaƙa da irin ayyukan da gwamnatin Nasir Idris ke aiwatarwa a fannoni daban-daban, ciki har da ilimi, kiwon lafiya, noma, hanyoyi, walwalar ma’aikata da ci gaban al’umma.

 

Ya ce gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen aiwatar da manufofin da za su amfani talakawa kai tsaye, lamarin da ya bayyana a matsayin babban dalilin da ya sa jama’a ke ci gaba da mara mata baya.

 

Kwamishinan ya kuma ƙalubalanci jam’iyyun adawa da su fito da ingantattun manufofi da hujjojin ayyukan da suka gudanar, maimakon dogaro da kalaman siyasa kawai.

 

Ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da samun gagarumin goyon baya a dukkan ƙananan hukumomi 21 na Jihar Kebbi, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris.

 

Daga ƙarshe, Hon. Yakubu Ahmed-BK ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar APC, magoya baya da sauran al’ummar jihar da su fito cikin lumana domin tarbar Shugaban Ƙasa.

 

Ya ce, “Saƙonmu a bayyane yake: Kebbi ta shirya, Kebbi tana da haɗin kai, kuma Kebbi tana tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC.”

 

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Gwamnan Jihar Kebbi Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Yahaya Sarki, ya fitar a ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba, 2026.