Daga GARBA MUHAMMAD

 

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta sake fasalin tsarin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Kwamitin Yakin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa, inda ta taƙaita ikon yin magana a madadin kwamitin ga manyan jami’ai uku kacal, a daidai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan wasu daga cikin kakakinta, musamman Alwan Hassan.

 

A wata sanarwa da kwamitin ya fitar, ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin tabbatar da haɗin kai, bin ƙa’idoji da inganta yadda ake isar da saƙonnin jam’iyyar ga jama’a gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

 

A sabon tsarin, mutane uku kaɗai aka amince su riƙa magana a madadin kwamitin, waɗanda suka haɗa da Darakta-Janar na Yakin Neman Zaɓen, Sanata Abdulaziz Yari; Ministan Ma’adanai, Dele Alake, wanda zai kasance kakakin kwamitin na hukuma; da kuma Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris.

 

Kwamitin ya umarci duk sauran mutanen da a baya aka sanar a matsayin kakakinsa da su koma ƙarƙashin Sashen Yaɗa Labarai da Sadarwa ta Dabaru a matsayin mambobi kawai, lamarin da ke nufin an cire musu ikon yin magana a madadin kwamitin.

 

Haka kuma, kwamitin ya buƙaci gidajen rediyo da talabijin su lura da wannan sauyi, yana mai bayyana cewa daga yanzu shi ne zai riƙa tantance mutanen da za su wakilce shi a shirye-shiryen kafafen yaɗa labarai idan buƙatar hakan ta taso.

 

Sanarwar na ɗauke da sa hannun Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, wanda kuma shi ne Mataimakin Darakta-Janar mai kula da harkokin gudanarwa na Kwamitin Yakin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC.

 

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta samun ce-ce-ku-ce kan kalaman Alwan Hassan, ɗaya daga cikin mutanen da a baya aka sanar a matsayin kakakin kwamitin, sakamakon wasu maganganu da ya yi a shirye-shiryen talabijin waɗanda suka jawo suka da martani daga jama’a.

 

A makonnin baya, Hassan ya tayar da ƙura bayan ya yi zargin cewa wasu ministoci na biyan biliyoyin nairori domin samun naɗin mukami, sannan bayan sun hau kujerar mulki su fara neman hanyoyin dawo da kuɗaɗen da suka kashe.

 

Hassan ya yi wannan zargi ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise News, a lokacin da yake kare nasarorin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin zaɓen 2027.

 

A yayin hirar, ya bayyana wasu nasarorin gwamnatin Tinubu a fannonin ilimi, wutar lantarki, fasahar zamani da biyan haƙƙoƙin ‘yan fansho, yana mai cewa waɗannan nasarori za su taimaka wa APC wajen sake ƙwato jihohin da ta rasa a zaɓen 2023.

 

Sai dai a ƙoƙarinsa na kare gwamnatin, Hassan ya yi zargin cewa wasu ministoci sun fi mayar da hankali wajen dawo da kuɗaɗen da suka kashe domin samun muƙamansu.

 

“Akwai ministoci da dama da suke biyan biliyoyin nairori domin a naɗa su muƙamai. Da zarar sun samu muƙaman, abu na farko da suke tunani shi ne yadda za su dawo da kuɗaɗen da suka kashe,” in ji Hassan.

 

Wannan furuci ya jawo ce-ce-ku-ce a faɗin ƙasar, lamarin da ya sa jam’iyyar APC ta fito fili ta nesanta kanta daga zargin.

 

Daga bisani, jam’iyyar ta musanta cewa ministocin gwamnatin Tinubu sun biya biliyoyin nairori domin samun naɗi, tana mai bayyana cewa kalaman Hassan na nufin wasu zarge-zargen abubuwan da suka faru a gwamnatocin baya ne, ba gwamnatin Tinubu ta yanzu ba.

 

A wani sabon lamari da ya ƙara jawo hankalin jama’a, Hassan ya sake shiga tsaka mai wuya bayan ƙoƙarinsa na nuna yadda lambar wayar neman agajin gaggawa ta 112 ke aiki a Najeriya ya ci tura a yayin wani shirin talabijin kai tsaye.

 

Lamarin ya faru ne ranar Talata yayin da Hassan yake ba da amsa a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels Television, wanda Seun Okinbaloye ke gabatarwa.

 

A lokacin hirar, Hassan ya bayyana lambar 112 a matsayin ɗaya daga cikin nasarorin gwamnatin Tinubu, inda ya ƙalubalanci mai gabatar da shirin da ya kira lambar a take domin nuna wa ‘yan Najeriya yadda za su iya samun agajin gaggawa.

 

“Ɗauki wayarka ka kira 112. Mutane da dama ba su san da wannan lamba ba. A da muna jin ana amfani da 911 a Amurka. Yanzu ka kira 112, ka kunna lasifika, za su tambaye ka irin agajin gaggawar da kake buƙata. Wannan duk godiya ce ga gwamnatin APC,” in ji Hassan.

 

Sai dai abin ya kasance akasin yadda ya yi zato, domin kiran da mai gabatar da shirin ya yi bai shiga ba.

 

“Wannan lambar ba ta aiki,” in ji Okinbaloye a yayin shirin.

 

Da yake mayar da martani, Hassan ya danganta rashin haɗuwar kiran da yiwuwar matsalar sadarwa, yana mai dagewa cewa lambar tana aiki, kuma shi kansa ya sha kiranta a baya cikin nasara.

 

Wannan lamari ya ƙara haifar da muhawara a tsakanin ‘yan Najeriya, musamman a kafafen sada zumunta, inda mutane suka yi ta bayyana ra’ayoyinsu kan yadda aka kasa samun haɗin lambar agajin gaggawa a yayin shirin kai tsaye.

 

Sai dai sanarwar sake fasalin kwamitin ba ta bayyana kai tsaye cewa rikicin lambar 112 ko kalaman Hassan kan ministoci ne suka haddasa sauyin ba.

 

Duk da haka, sabon tsarin ya mayar da ikon magana a madadin Kwamitin Yakin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC hannun jami’ai uku kacal, yayin da sauran tsoffin kakakin kwamitin za su ci gaba da aiki a matsayin mambobin sashen yaɗa labarai da sadarwa ta dabaru.