Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya saka gwamnonin hamayya biyu cikin kwamitin yaƙin neman zaɓensa na 2027. A ranar Laraba ne za a ƙaddamar da kwamitin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Gwamnonin hamayyar da suka samu shiga kwamitin yaƙin neman zaɓen su ne Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord, sai kuma Charles Soludo […]
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya saka gwamnonin hamayya biyu cikin kwamitin yaƙin neman zaɓensa na 2027.
A ranar Laraba ne za a ƙaddamar da kwamitin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Gwamnonin hamayyar da suka samu shiga kwamitin yaƙin neman zaɓen su ne Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord, sai kuma Charles Soludo na jam’iyyar APGA.
Baya ga gwamnonin biyu, kwmaitin ya kuma saka Ministan Abuja Nyesom Wike na PDP cikin kwamitin, inda aka naɗa shi kodinetan Abuja da Rivers.
Haka ma akwai tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanata a jami’yyar PDP, Ibrahim Danƙwambo, wanda aka bai wa muƙamin mai bayar da shawar a kwamitin.
Wannan ba abu ne da aka saba gani ba a siyasar ƙasar.
Da yake jawabi game da batun, Ministan Abuja Nyesom Wike ya ce matakin ya nuna wayewar Shugaban Tinubu na APC a siyasance.
”Hakan na nuna burin shugaban ƙasar na haɗa kan mutane, har daga wajen jam’iyyarsa ta APC”, in ji tsohon gwamnan na jihar Rivers.
